Shirin na International Institute for Tropical Agriculture ko IATA zai maida hankali ne akan inganta noman shinkafa da dawa da rogo.
Shirin ya samu goyon bayan bankin raya kasashen Afirka wanda kuma shi ne yake samar da kudaden kaddamar da shirin tare da cibiyar binciken tsirai a kasashe masu zafi da cibiyar noman shinkafa a Afirka da ma'aikatar noma ta Najeriya nada zummar samar da isasshen abinci da ayyukan yi.
Injiniya Haruna Akwashiki wanda yake kula da shirin a Najeriya yana mai cewa tsari ne na musamman na horas da matasa kan aikin gona.
Yace a karkashin shirin ana gina cibiyoyi ukku da zasu horas da matasa dubu dari ukku akan aikin gona. Ya kara da cewa irin cibiyar ce aka kaddamar yau kuma shi ne irinsa na farko da aka taba kaddamar wa a Najeriya.
Daraktan bakin raya Afirka a Najeriya Mr. Ebimafa yace su ma suna mara wa shirin baya. Yace goyon bayan da bankin ke ba aikin gona a Najeriya yayi daidai da tsarin gwamnatin kasar na inganta ayyukan gona. Yace kimanin dalar Amurka miliyan dari da hamsin ne suke niyyar kashewa a yankunan a Adani da Omuwo da Bidda da Badeji da Kebbi da Sokoto da kuma Kano da Jigawa.
Injiniya Husseini Hassan kwararre akan harkokin aikin gona a Najeriya yace shirin yana da mahimmanci kwarai da gaske. Mahimmancin farko shi ne horon da za'a ba matasa da zai sa su san aikin da zasu yi. Na biyu za'a iya ba matasan bashi su bunkasa ayyukansu. Na ukkun shi ne yiwuwar yawaitar abinci a kasar. Lamarin zai sa farashin abinci ya sauko. Ana kuma iya kai abincin kasashen waje.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum