Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Za Ta Dauki Matakiin Maida Martani A kan Shirin Karin Harajin Amurka


Kasar China ta dauki alkawarin daukar matakin maida martani akan shirin Shugaban Amurka Donald Trump,na kara haraji akan kayayyakin dala biliyan dari biyu da za’a rika shigowa dasu daga China.

Sabon harajin wanda zai fara aiki a ranar Litinin, ashirin da hutu 24 ga watan satumba , zai fara da kashi 10 cikin dari sannan ya karu zuwa kashi ashirin da biyar daga cikin dari a watan janairun shekarar 2019, idan Allah ya kaimu.

Za’a aza harajin ne akan dubban kayayyakin amfani wadanda suka hada da na'urorin wutar lantarki, da kayayyakin abinci,da kayan aiki da kuma kayan amfanin gida.Gwamnatin Ttrump ta cire wasu kaya masu yawa daga cikin kayan da aka sakawa sabon harajin wadanda suka hada da agogon hannu, da na’urar Bluetooth da kuma kujerar zaman yara a cikin mota.


Ma’aikatar kasuwancin China, ta fitar da wani bayani a yau talata tana gargadin cewa zata maida martani akan sabon harajin da aka aza mata don kare hakkinta da muradun ta da kuma yarjejeniyar duniya na yancin gudanar da harkokin cinikayya babu tsangwama. Tunda farko China ta gabatar da jerin sunayen kayayyakin Amurka na dala biliyan sittin , da zata karawa haraji don maida martani akan Karin harajin da Amurka da ta yiwa kayayyakin da take shigo dasu..

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG