China ta ce wani jirgin ruwan jigilar matafiya, wanda ke kokarin ratsa kogin Yangtze dauke da mutane sama da 450, ya nitse daren jiya Litini a yankin Hubei na tsakiyar Chinar.
Bayanan farko-farko da aka samu daga kamfanin dillancin labaran China na Xinhua ba su wadatar ba. Kafar labaran ta ce jirgin mai suna Dongfanghizing, wato Tauraron Gabas, ya taso ne daga Nanjing zuwa birnin Chongqing a Kudu maso Yammacin China.
Take dai babu bayanai kan wadanda abin ya rutsa da su.
Kafar ta Xinhua ta ce an ceto keftin din jirgin da babban injiniyan, kuma dukkansu sun ce cikin kankanin lokaci jirgin ya tintsire sanadiyar abin da kafar labaran ta kira mahaukaciyar guguwar ruwa.
An tsamo mutane 8 daga cikin ruwan, yayin da ake shirin kai dauki safiyar yau Talata.
Rahoton ya ce iska mai karfi da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya sun kawo cikas ga yinkurin ceto mutanen.
Kamfanin dillancin labaran ya ce Premier Li Keqiang da kansa ne zasu sa ido kan ayyukan ceton, kuma tun da safiyar yau Talata ya kama hanyar zuwa wurin ayyukan ceton tare da tawagar ayyukan ceto daga Babban Kwamitin Kasa.