Jaridun Najeriya da dama a yau Litinin sun ruwaito cewa shugaban ‘yan sandan kasar, Ibrahim Idris, ya nemi Kassim Afegbua, kakakin tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida, da ya mika kansa cikin sa’o’i 24 ko kuma a kama shi.
Umurnin na zuwa ne yayin da ake zargin Afegbua da rubuta wata sanarwa da yawun Babangida ba tare da izninsa ba.
Shi dai Afegbua ya kwashe sama da shekaru goma yana magana da yawun tsohon shugaban, kuma ya musanta rahotanni da ke cewa 'yan sanda sun ce a kama shi.
"Babu wani batu kamar haka da ke cewa 'yan sanda sun ce a kama ni." Inji Afegbua, kamar yadda jaridar yanar gizo ta Premium Times ta wallafa.
Sanarwar da ya fitar a ranar Asabar a madadin Babangida, ta yi nuni da cewa Babangida ya nemi shugaba Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takara a zaben 2019.
Sai dai ba tare da bata lokaci ba, tsohon shugaban ya musanta fitar da wannan sanarwar, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da ita.
“Ina da hanyar da zan tuntubi shugaban kasa ba tare da wata matsala ba, ba sai na fito na yayata matsayata a baina jama’a ba.” Babangida ya fada a wata sanarwa da ya fitar bayan bayyanar ta Afegbua.
Amma a wata hira da ya yi da gidan talbijin din Channels a baya, Afegbua ya ce yana kan bakarsa kan cewa da yawun tsohon shugaban kasar ya fitar da wannan sanarwar.
Wannan lamari ya janyo ka-ce-na-ce- a tsakanin 'yan siyasa da masana kan wa ke da gaskiya a wannan lamari.
Wannan takaddama har ila yau na zuwa ne, kasa da makwanni biyu bayan da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar da wata sanarwa, wacce ta nemi shugaba Buhari da kada ya tsaya takara a shekarar 2019.
Ita ma wannan wasika ta haifar da cece-ku-ce a tsakanin al'umar Najeriya inda aka yi tsokaci na nuna goyon bayan Obasanjo da kuma akasin haka.
Facebook Forum