Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Castro: Shugabannin Duniya Na Ci Gaba Da Bayyana Ra'ayoyi Mabanbanta


Marigayi Fidel Castro
Marigayi Fidel Castro

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da tsokaci game da rasuwar tsohon shugaban Cuba Fidel Castro, wanda ya rasu a karshen makon nan yana mai shekaru 90.

Wasu daga cikin shugabanin sukan yabe shi ne, yayin da wasu kuma suke sukar shi.

A baya-bayan nan Firai ministan Canada, Justine Trudeau, ya kwatanta Castro a matsayin wanda ya nuna kauna ga al’umarsa ta Cuba, tsokacin da ya janyo suka daga ‘yan siyasar kasar ta Canada da ma na nan Amurka.

Firai minister Trudeau, wanda ya ziyarci Cuba a ‘yan watannin da suka gabata, ya ce duk da cewa Castro mutum ne mai cike da takaddama, masu yabonsa da sukarsa sun amince cewa, ya nuna kauna da kishin jama’ar kasarsa.

Wasu da dama suna ganin rasuwar Castro ba lallai ne ta samar wani sauya a fagen siyasar kasar ta Cuba ba.

“Fidel Catro ya jima da barin ofis, tuni aka mika mulki zuwa ga Raul Castro, amma shin za a samu wani canji yanzu tunda Castro ya rasu? Koda ya ke ina ga wannan wani nauyi ne da ya kamata a sauke.” In ji Ilean Ros-Lehtinen, ‘yar majalisar dokokin jihar Florida.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump ya kwatanta Fidel Castro a matsayin “Mugun shugaba” wanda ya muzgunawa jama’arsa.

XS
SM
MD
LG