Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cacar Baki Ta Barke Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Ta Jihar Zamfara Game Da Sulhu Da ‘Yan Bindiga


Dauda Lawal
Dauda Lawal

Gwamnatin jihar Zamfaran ta nemi gwamnatin Tarayya ta mata karin bayani kan zaman sulhu da yan bindiga cikin sirri da wasu jami’anta ke yi a jihar ba tare da saninta ba ko ma jami’an tsaron da ke jihar.

Gwamna Jihar Zamfara Dauda Lawal yau Talata, ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga.

A shekaran jiya ne Ministan na labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro. Biyo bayan neman ƙarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ƙarƙashin ƙasa da ‘yan bindiga.

A wata takardar bayani, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tada hankali da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga.

Ya ƙara da cewa Ministan na Labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yanke wa gwamnatin Zamfara hanzari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Zamfara ba tare da sanin Gwamnatin Jiha ko shugabanni jami’an tsaron jihar ba.
“Muna da gamsassun hujjoji dake tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindiga a wurare mabambanta a Zamfara.


“Akwai ban takaici a ce Ministan Yaɗa Labarai zai fito bainar jama’a ya kore batun ba tare da ya nemi sani daga jami’an tsaro ko ‘yan uwanshi da ke da hannu dumu – dumu a lamarin ba. Mun tsammaci tunda ƙwararre ne a harka yada labarai, zai bi matakan da ilimi ya sharɗanta don tabbatarwa ko kore batun namu.


“Gwamnatin Jihar Zamfara tana matuƙar mutunta ƙa’ida tare da ganin ƙimar hukuma. Ba za mu fito kafafen watsa labarai muna fallasa sunayen jami’an Gwamnatin Tarayyan da ke wannan ta’asa ba, amma mun sanar da ‘yan Nijeriya don su nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin ta Tarayya.

“Muna so mu sanar da Minista cewa jami’ansu na Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar wannan zaman sulhu da ‘yan bindiga, sune ke siyasantar da matsalar tsaro, ba Gwamnatin Zamfara ba.

“Ba mu san daga inda Ministan ya samu ƙwarin gwiwan bugun ƙirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi waɗannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.

“Muna sake nanatawa cewa sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da qarfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.

To sai dai kuma a martanin da ta mayar Gwamnatin Tarayya ta zargi gwamnatin jihar zamfara da siyasantar da batun tsaron.

Ministan watsa Labaran Najeriya Idriss Malagi ya ce kalaman na gwamnatin Zamfara ya ba shi kunya ganin Jim kadan da faruwa al’amarin aka dau matakin gaugawa don kubutar da daliban.

Malagi ya ce maimakon Gwamna Dauda Lawal ya godewa Hukumomin gwamnatin Tarayya saboda hobbasan ceto daliban amma sai ya buge da sa siyasa a cikin al’amarin.

Yace ko kadan ba wani jami’in gwamnatin Tarayya da ke wani tattaunawar Sirri da yan bindiga a zamfara.

Wannan ce ce ku ce dai a cewar masanin tsaro Dr Kabiru Adamu yan bindigar ne za su ci moriyarsa inda ya bukaci bangarorin biyu su yi taka tsantsan.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG