Taron shugabannin kasashen Africa ta gabas wanda akayi a Arusha na kasar Tanzania, jiya Laraba, ya bayyana tsohon shugaba Mkapa dan shekaru 77 a matsayin wanda zai jagoranci tattaunawar da ake sa ran ta kai ga zaman lafiya.
Da farko Shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni ne aka dankawa wannan aikin amma hakan bai cimma nasara ba.
An jiwo Pancras Cimpaye mai Magana da yawun hukumar samar da zaman lafiya ta yarjejeniyar Arusha na cewa ba shakka tsohon shugaba Mkapa yana sane da batutuwan samar da zaman lafiya na yarjejeniyar Arusha, don haka muna fata zaiyi duk abinda ya dace domin ganin wannan tattaunawar takai ga nasarar da take bukata.
Sai dai Cimpaye yace ba kanshin gaskiyar dake cewa wai an dakatar da shugaba Yuweri Museveni daga cikin maganar saboda rudanin da aka samu a zaben da aka gudanar a kasar tasa ta Uganda.