Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai ya jagoranci bikin share gari da sojoji ke yi kowace shekara. A wannan karon, rundunar da gudanar da bikin a garin Gudumbali da sojoji suka kwato daga kungiyar Boko Haram wanda 'yan garin suka koma a kwanannan bayan shekaru bakwai.