Tun da sanyin safiyar yau Alhamis ne manya da kananan jiragen yakin Najeriya su ka yi ta kaiwa da komowa a sararin samaniyar Birnin Abuja.
Abin da Babban Hafsan Sojojin kasar ke cewa hakan gaisuwa ce ga 'yan mazan jiya da suka sadaukar da rayuwarsu don Najeriyar.
Masanin tsaro Farfesa Mohammed Tukur Baba ya ce cikin shekaru sittin din da kasar tai da 'yancin kai, an yi ta fama da matsalolin tsaro iri iri, kama daga Juyin milki na farko zuwa yakin basasa, Rikicin maitatsine a biranen Kano, Maiduguri, Yola, Gombe da wasu sassan jihar Kaduna.
Tun dai bayan yakin basasa, babu wata fitina da ta girgiza Najeriya irin tarzomar Boko Haram da a halin yanzu ke shiga shekara ta goma sha daya.
Kodayake masana harkar tsaro irin su Dr. Kabiru Adamu na ganin cikin shekaru sittin dinnan a iya cewa an sami nasara duk kuwa da yan matsalolin da ba a rasa ba, musamman ganin duk da rikice rikicen da ta fuskanta kasar na nan a dunkule.
Lokacin rantsuwar kama mulki a wa'adi na farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin maida cibiyar bada umarnin yaki zuwa Maiduguri har sai an kawo karshen Boko Haram.
Buhari yace ba za ace an dakile Bokon Haram ba har sai an ceto baki dayan 'Yan matan Chibok da ma duk mutanen da yan ta'adda ke rike dasu.
Kodayake ra'ayoyin Yan Najeriya da ma kwararru ya banbanta dangane da ko an sami ci gaba a yaki da Boko Haram da kuma batun matan na Chibok.
Amma dai abune sananne cewa har yanzu Boko Haram na rawar gaban hantsi a Jihar Borno da ma sassan Arewa maso gabas. Domin sau uku ana kai hare hare kan tawagar gwamnan jihar Borno Engineer Babagana Zulum, al'amatin da masana tsaro ke cewa da sauran aiki Ja.
Yanzu dai abin jira a gani shine yadda shugaba Muhammadu Buhari zai shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar ta ko'ina.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Facebook Forum