Za’a yi wani zaman tattaunawar da ba a hukumance ba tsakanin ‘yan Taliba da gwamnati da kungiyoyin rajin zaman lafiya Doha babban birnin Qatar. Pakistan ta ce a shirye take ta goyi bayan yunkurin da zai kawo zaman lafiya a Afghanistan makwabciyarta.
A halin da ake ciki yanzu ana shari’ar wasu mutanen Afghanistan guda 49, ciki har da ‘yan sanda guda 19 da ake zargi da hannu a dukan taron dangin da aka yiwa wata mace ‘yar shekaru 27 da yayi sanadiyyar rasa ranta a watan da ya gabata bisa zargin ta wulakanta Al’kur’ani mai tsarki.
Zaman shari’ar da aka fara a jiya tare da nunawa a talbijin a inda masu gabatar da kara suke gardamar cewa ita Farkhunda ta sha dukan da yayi sanadiyyar mutuwarta da kone ta ne sakamakon zargin ta wulakanta Alkur’ani mai tsarki.
Mafi yawancin ‘yan sandan dai ana zarginsu ne da sakacin daukar matakin hana faruwar lamarin, duk da yake dai ana zargin wasunsu da sa hannu wajen aikata kisan.