Dubban masu goyon bayan shugaban ne suka yi ta tururuwa akan titin zuwa filin saukar jiragen sama na Abuja, domin yin lale marhabin da shugaba Muhammadu Buhari wanda ya tafi jinya tun a ranar 7 ga watan Mayu.
Shugaba Buharin ya dawo kasar ne a jiya Asabar bayan da ya tsawaita zaman jinyar ta sa, wacce ba a bayyana takamaimai me ke damunsa ba.
Lamarin da ya sa wasu suka yi ta kiran da ya dawo gida ko kuma ya sauka a mulki.
Mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya rike mukamin mukaddashin shugaban kasa, na daga cikin wadanda suka tarbe shi a filin tashin jiragen na Abuja.
A watan Janairun wannan shekara Buhari ya fara tafiya zuwa kasar ta Burtaniya neman magani, inda ya kwashe kusan watannin biyu yana jinya, sannan ya komo gida a watan Maris.
Amma kuma a farkon watan Mayu ya sake komowa.
A lokacin da zai tafi neman maganin, shugaba Buhari ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
A farkon makon da ya gabata ne kuma wasu masu zanga zanga a birnin Abuja suka tsaurara fafutikar neman shugaban ya dawo gida ko kuma ya yi murabus, inda a jihar Legas ma aka yi makamanciyar wannan zanga zangar.
Facebook Forum