Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki Kan Matsalolin Nijeriya, Lokacin Da Ya Je Adamawa


Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.
Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.

Dan takarar Shugabancin Nijeriya karkashin jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, wanda ya je yakin neman zabe a jihar Adamawa, ya ce lallai zai dau mataki kan jerin matsalolin da ke addabar Nijeriya.

A yakin neman zaben da ya je yi a Yola, babban birnin jihar Adamawa, dan takarar shugabancin Nijeriya karkashin jam’iyyar APC kuma tsohon Shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari ya ce lallai gwamnatin APC za ta magance matsalolin tsaro wanda a halin yanzu ma ana takaddama kan makomar wasu kananan hukumomi akalla biyu ba jihar Adamawa; wasu kuma noma su ka yi amma sun kasa girbi; wasu kuma an raba su da iyalansu , kuma ‘yayansu bas u makaranta. Don haka Allah ya sauwake ma jama’a irin wannan bala’in.

Tuni wasu kososhin jam’iyyar ta APC a wurin yakin neman zaben su ka yi ta kiran da su ka saba na a kada kuri’a a tsare a raka a kuma jira sakamako cikin kwanciyar hankali. Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’a da su fito su zabi abin da ya kira, “APC sak,” saboda ci gaban kasar. Ya ce a kada kuri’a a raka sannan a jira sakamakon zaben. Wata shugabar mata mai suna Ambassada Fati Balla ta ce wasu ‘yan yankin da dama sun bar garuruwansu saboda rikicin Boko Haram. Ta ce muddun Janar Buhari ya zama Shugaban kasa to za a magance matsalolin.

Wasu daga cikin wadanda su ka halarci gangamin yakin neman zaben sun ce sun yi imanin cewa Buhari zai magance matsalolin Nijeriya. Hasalima, akwai wanda y ace ya na jira ne matarsa da ke da ciki ta haihu ya sa ma dan suna Buhari matukar na miji ne.

Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki Kan Matsalolin Nijeriya, Lokacin da Ya je Adamawa - 3'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG