Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murnarsa ga dan takarar jam’iyyar APGA Farfsesa Charles Soludo wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Anambra.
Soludo ya sami kuri’u dubu 112, 229, abin da ba shi damar ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jam’iyyar PDP da ya sami kuri’u dubu 53, 807, da kuma Andy Uba na jam’iyyar APC, wanda ya sami kuri’u dubu 43, 285.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, Buhari ya yi kira ga Soludo da ya hada kan masu ruwa da tsaki don magance matsalolin da ke fuskantar jihar da yankin kudu masu gabashin Najeriya.
Shugaban ya kuma nuna sha’awarsa ta ganin sun yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Anambra da Najeriya baki daya.
Buhari ya kuma yabawa jami’an tsaron da suka tsaya tsayin-daka wajen ganin zaben ya gudana lami lafiya.
Ya kuma jinjinawa hukumar zabe ta INEC bisa kokarin da suka yi wajen gudanar da zaben duk da kalubalen da aka fuskanta a baya.