Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Roki Musulmai Su Ciyar Da Talakawa Yayin Da Ya Ke Marhaban Da Azumin Ramadan


Shugaban ya shawarci attajirai Musulmi da su guji almubazzaranci, yayin da wasu ke fama da yunwa da fatara.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen tarbar watan Ramadan, watan da Musulmai ke tsawaita ibada.

A cikin wata sanawar da Buhari ya fitar ta hannun Kakakinsa, Malam Garba Shehu, Shugaban ya aike wa 'yan Najeriya da ma Musulmi a duk fadin duniya, sakon cewa wannan lokaci ne da ke ba da dama ta musamman na ''jin yunwar da talakawa ke fama da ita''.

Shugaban ya shawarci attajirai Musulmi da su guji almubazzaranci yayin da wasu ke fama da yunwa da fatara, inda ya bukaci da su kula da makwabtansu, talakawa da marasa galihu.

Ya kuma yi kira da a yi addu’o’in samun zaman lafiya a kasar nan da ma wajenta, da kuma samun lafiya da zaman lafiya a fadin duniya.

Ya kara da yin fatan kammala azumin kwanaki 30 cikin nasara.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG