Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar Sheikh Abubakar Tureta a matsayin wani babban rashi da zai bar gurbi a fagen ilimi.
A wata sanawar da fadar shugaban kasar ta fitar a yau Litinin, kan rasuwar Sheikh Tureta, wacce kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai san zaman lafiya.
“Ya kwashe shekarunsa yana yada sakonnin zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban.” Inji sanarwar.
Buhari ya kuma yi kira ga sauran malaman addini da dalibansa da su rika koyi da abin da ya koyar yana mai fatan Allah ya mai rahama.
“Iya bakin rayuwarsa, ya yi kokari ya kauce wa riginginmu masu raba kawunan jama’a, tare da nuna kyama ga masu yada kalaman batanci.”
Sheikh Abubakar Tureta, wanda fitaccen Malami ne, ya rasu yana da shekaru 74 a Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya.
A yau Litinin aka yi jana’izarsa a jihar ta Kaduna.
Facebook Forum