Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Lashe Zabe A Mazabar Atiku


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Dimbin magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan takarar shugaban kasa a jami'iyyar APC sun bayyana matukar farin cikin su da nasara ya yi a mazabar abokin karawarsa dan takarar PDP Atiku ABubakar.

Bayan kirga kuri'a a runfar zaben Atiku ta Ajiya Unit 012, shugaba Buhari ya samu kuru'u 186, yayin da madugun 'yan adawan Atiku Abubakar ya samu kuru'u 167. Ratar kuru'u 19 ya baiwa shugaba Buhari na APC nasara a wurin.

To ko yaya jam’iyar PDP ta ji da wannan kaye a runfar ta Atiku? Alhaji Yahyaji Gombi wakilin jam’iyar PDP a wannan runfar ya tattauna da Muryar Amurka.

Yanzu dai ana cigaba da hada hancin sakamakon zaben da aka yi,zuwa shedikwatar hukumar zabe na jihohin biyu.

Ga dai Ibrahim Abduaziz da karin bayani a cikin wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG