Aikin wannan kwamiti shine yin nazari, da tacewa akan duka rahotanni masu yawan gaske da gwamnati mai barin gado ta shirya, da kuma sa ido a wadansu ayyukan shi shugaba mai jiran gado ya baiwa kwamitin.
Daya daga cikin ‘ya’yan wannan kwamiti Barrista Solomon Dalung yayiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani akan ayyukan da aka basu.
“Zamu yi nazari, sai kuma mu fidda bayanai bisa akan ko mene ne yake kunshe domin amfanin gwamnati mai zuwa. Sannan kuma bayan wannan, aikin ya umarce mu zana wa wannan gwamnati mai zuwa tsari da zai kasance makomanta”.
A zaben ran 28 ga watan Maris ne Jam’iyyar PDP dake rike da mulkin Najeriya na tsawon shekaru 16 ta sha kashi a hannun jam’iyyar adawa ta APC. Bugu da kari, APC ta kwace kujerun gwamnoni da na ‘yan majalisu a duk fadin Najeriya a babban zaben da aka kamala a baya-bayannan.
Wannan shine karo na farko a tarihin Najeriya da jam'iyyar dake kan mulki ta sha kashi, kuma take shirin mika mulki ga jam'iyyar adawa.