Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mu Hada Kanmu A Filato, In Ji Shugabannin Addinai


Shugabannin addinai (File Photo)
Shugabannin addinai (File Photo)

Shugabannin addinai sun ba gwamnati mai jiran gado a jihar Filato da ta mayar da hankali akan inganta rayuwar da hain kan al'umma.

Shugabannin sun kuma kira al'umma da su ba gwamnatin da zata kama mulki goyon baya domin ta samu nasara, kasa kuma ta cigaba.

Sheikh Alhassan Said na kwamitin amintattu na kungiyar IZALA ya fara da kiran shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Yace yana yiwa 'yan Najeriya murnar nasarar da Janar Buhari ya samu na zama shugaban kasa. Ya yiwa al'ummar Filato murna da canjin bazata da Allah ya kawowa jihar.

Jihar ta yi shekaru 16 tana fama da tashe-tashen hankula. Yanzu Allah ya kawo canjin gwamnati da suke sa ran an kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula.Yayi fatan Allah ya sa mutanen Filato su dinke su zama tsintsiya madaurinki daya, masu kaunar juna kamar yadda ake da can. Ya yiwa Najeriya addu'a Allah ya bata bunkasar arziki da kwanciyar hankali. Yace burin 'yan Najeriya nada yawa akan sabuwar gwamnatin saboda haka a yi masu addu'a Allah ya taimakesu su cika burin.

Shi ma shugaban kungiyar kiristoci ko CAN Rabaran Soja Bewarang ya bukaci shugabannin da su yi kokarin hada kawunan 'yan jihar domin a samu zaman lafiya da zai dore. Ya fara da godewa Allah da ya sa aka yi zabuka lafiya.

Yace Filato ta samu kanta a wani hali mai wuya amma mutane sun hada kai kuma Allah yayi abun al'ajabi da ya sa aka zabi Lalong da Tyoden su shugabanci jihar. Saboda haka kamata yayi shugabanni su sani yanzu babu banbancin addini ko kabilanci domin jihar ta cigaba. Su yi abun da zai nuna zaman tare a Filato. Su rike kowa da kowa. Su yi yadda jama'ar Filato zasu san basu sha wahala banza ba.

Ya kira sabuwar gwamnatin ta buba makarantun jihar da yace sun zama abun tausayi. Haka ma asibitoci duk sun durkushe, su ma a dubasu a ingantasu. Ya kira jama'a a yi rayuwa da tausayi, a bada goyon baya a hakura da juna. A manta da banbance banbance. A yi tafiya tare a kuma gafartawa juna.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG