Dubun dubatar mutane ne ke jibge a sansanoni daban daban a duk fadin jihar ta Borno, wadanda suka tsere daga gidajensu domin gujewa rikicin Boko Haram.
Kungiyar ta Boko Haram ta kwashe kusan shekaru da dama ta na kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya da ma kasashe ketare.
A ‘yan makwannin an samu korafe-korafen cewa wasu daga cikin wadanda ake dorawa alhakin raba kayan abinci da gwamnati da kungiyoyi ke aikawa ‘yan gudun hijrar suna sace kayan abincin.
Wannan lamari kuma ya sa a makon da ya gabata ‘yan gudun hijrar da dama suka yi zanga zanga.
Matsalar karancin abinci musamman mai gina jiki, ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a sansanonin ‘yan gudun hijrar, musamman ma kananan yara.
Domin jin fashin baki kan wannan batu, saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Umar Faruk Musa: