Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil Ta Dakatar Da Ayyukan Kamfanin Mai Na Chevron


Hoton tsiyayar man kamfanin Chevron a wani yankin tekun da gwamnatin Rio de Janeiro ta dauka ta jirgin sama
Hoton tsiyayar man kamfanin Chevron a wani yankin tekun da gwamnatin Rio de Janeiro ta dauka ta jirgin sama

Hukumar albarkatun man kasar ce ta fada ranar Laraba cewa an haramtawa kamfanin Chevron hakar mai

Hukumomin kasar Brazil sun dakatar da ayyukan hakar man da katafaren kamfanin Amurka na Chevron ke yi a kasar, bayan wata tsiyayar mai kwanan nan a gabar tekun jahar Rio de Janeiro.

A jiya Laraba hukumar albarkatun man kasar ta bayar da sanarwar cewa an haramtawa Chevron hakar mai har sai an samu cikakken bayani game da dalilan da suka jawo tsiyayar man.

An yanke wannan shawara ce kwanaki biyu bayan, gwamnatin kasar Brazil ta tilastawa Chevron biyan tarar dola miliyan 28 saboda tsiyayar man kuma, kuma ta ce kamfanin zai iya fuskantar biyan wata tarar a 'yan kwanakin da ke tafe nan gaba. Haka kuma jami'an gwamnatin kasar Brazil sun ce gwamnati za ta bukaci Chevron ta biya wasu kudade saboda bannar da tsiyayar man ta yi a kusa da kadadar man Frade. Tsiyayar man ta wakana ne a lokacin da Chevron ke hakar mai a wata rijiyar gwaji a kimanin tazarar kilomita 370 a gabar arewa maso gabas da Rio.

A jiya Laraba shugaban kamfanin a kasar Brazil, George Buck, ya roki gafarar 'yan majalisar dokoki saboda tsiyayar man, wadda masu saka ido suka ce an sha kan ta.

Chevron ya ce karfin man dake takure a cikin rijiyar gwajin ya zarce kiyasin da yayi nesa ba kusa ba. Chevron ya dauki laifin tsiyayar mai, yace a ranar takwas ga watan Nuwamba aka gano matsalar kuma cikin wasu 'yan kwanaki aka sha kan ta. Amma duk da haka dai Chevron yayi watsi da zargin cewa bai gaggauta sanar da hukumomin kasar ba ballantana kuma ya tsaftace inda man ya tsiyaya da kyau kamar yadda ya kamata.

An kiyasta cewa tsiyayar man ta haifar da zubar gangar mai 200 zuwa 300 a kowace rana cikin tekun Atlantika har tsawon mako daya ko ma fiye da makon daya.

XS
SM
MD
LG