Suna fushi ne saboda irin matakan da Shugaba Jair Bolsonaro ya dauka kan annobar, su ka yi ta ajiye gicciye a harabar ginin Majalisar Dokokin Tarayyar kasar a Brasilia, babban birnin kasar, don juyayin mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka.
Masu zanga zangar, ciki har da mambobin kungiyoyin ma’aikata, da ‘yan asalin kasar, da kungiyar ‘yan luwadi da madigo, sun rubuta takardar hadin gwiwa ga Majalisar Dokokin kasar ta bukatar tsige Shugaban.
Bolsonaro ya sha suka saboda yadda ya yi ta shiriritar da barazanar annobar. Shugaban ‘yan asalin kasar, Kretan Kaingang ya ce wani dalilin zanga-zangar kuma shi ne karrama wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar cutar corona.
Facebook Forum