Kasar Botswana za ta fara sassauta dokar hana zirga-zirga ta makwanni biyar sannu a hankali, domin takaita yaduwar cutar coronavirus a ranar Juma’a.
Mataimakin shugaban kasar Slumber Tsogwane ya ce, bisa la’akari da irin matakin da gwamanti ke dauka akan barkewar annobar coronavirus da kuma irin yanayin cutar, gwamanati ta yanke shawarar bude tattalin arziki sannu a hankali, yayin da take lura da yanayin cutar.
Tsogwane ya yi wannan sanarwar jiya Laraba, a lokacin da ya tattauna da 'yan majalisar da suke duba bukatar shugaban kasar Mokgwetsi Masisi kan sake bude makarantu da tattalin arziki.
Shugaba Masisi ya zabi bin matakan tsarin da ya dace da ka’idodin da jami’an kiwon lafiya suka shata na a ci gaba da kula da takaita yaduwar coronavirus.
Masisi da 'yan majalisar sun saka kyallayen rufe fuska a lokacin tattaunawar. Batswana dai ta tabbatar da mutane 28 da suka kamu da coronavirus, kana daya ya mutu.
Facebook Forum