Wasu jiragen Soja sunyi shawagi a rewacin jihar Adamawa, inda suka watso wasu kasidu dake ikirarin cewa mayakan Boko Haram, na nadamar abubuwan da suka aikata.
Wasu mazauna garin Gombe, da aka watso takardun cikin gidajen su sun ma bayyana cewa kasidun an rubuta sune acikin harsunan Hausa, Turanci dama harshen larabci. Lamarin dai ya jefa jama’a cikin firgita da rashin sanin tabbas. Wasu mazuna garin dai sun bayyana cewa jiragen soja ne ke shawagi a sararin sama suna jefo takardu kasa har cikin gidajensu, sai mutane suka rinka daukar takardun suna karantawa, sakon dai nace ‘yan Boko Haram suna nadamar abubuwan da sukayi.
Baya dai ga karamar hukumar Gombe, haka nan ma an watsa irin wannan ‘kasidu a yankin Sun, kamar yadda wani jami’in karamar hukumar daya nemi a sakaye sunan sa ya shaidawa wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz, yace jiragen sojoji ne suke ta zagayawa cikin gari sun ta jefa takardun kota ina, yakuma ce jama’ar gari hankulan su a tashe yake amma ya sanarwa da shugaban karamar hukumar, wanda har yayi magana da jami’an tsaro a Yola, domin tabbatar da cewa shin sojoji ne da gaske suke raba takardun.
Kawo yanzu dai hukumomin sojoji a jihar basuyi karin haske ba. Yayin da a ‘bangare guda kuma masana harkar tsaro suke ganin akwai bukatar karatun ta nutsu ga wannan batu. Mallam Muhammad Abudulhamid na cibiyar cigaban al’umma yama aza ayar tambaya game da irin wadannan kasidu da ake rabawa, inda yace, “dayawan mutane suna ganin wannan abu kamar shiryawa ma akayi, sai ya zamanto kamar su jami’an tsaro na Najeriya, abubuwan da suke yi sai ya zamanto kamar in suna haka zai bada dama ga jama’ar gari suga kamar sojojin Najeriya suna kokari, kuma yakamata a fito ayi ta musu addu’o’i da dai sauransu. Haka suke fitowa suce sun kashe Shekau sai daga baya ya fito yayi magana, dole ne ayi taka tsan tsan.”
Duk wannan lamari na faruwa a yayin da shedikwatar tsaron Najeriya, a ban gare guda ke bayyana irin nasarorin da ake samu a yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram din.