Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, sun far ma wasu kauyuka da ke kan hanyar shiga birnin Maiduguri inda suka kashe akalla mutum takwas.
Wakilin Muryar Amurka da Haruna Dauda Biu, wanda ya ziyarci wasu daga cikin kauyukan, ya aiko da rahoton cewa maharan sun yi kone-kone tare da wawure kayayyakin abinci da dama.
Kauyukan da aka kai harin sun hada da Kofa da Kolomti da Gomari da kuma kauyen Gwazari.
An kai harin ne da misalin lokacin sallar Isha’i “bayan mun tashi daga sallar Isha’i ba mu samu damar komawa gida ba, da rarrafe ma muka fita daga garin.” Inji wani mazaunin garin a hirar da ya yi da Muryar Amurka.
A lokacin hada wannan rahoto, hukumomi tsaro ba su ce uffan dangane da adadin mutanen da suka rasu ba.
Amma wata sanarwa da mai tsare-tsaren hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA a Arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Bashir Garga ya fitar, ta nuna cewa maharan sun shiga kauyukan ne cikin wasu motoci hudu da babura da dama, inda suka rika kai hare-hare.
Facebook Forum