Shugabanin addanin Islama a Najeriya sun yi kira da a dukufa wajen yin addu’oi domin ganin an kawo karshen tashin hankalin hare-haren kungiyar Boko Haram.
Malaman sun yi kiran ne yayin da ake addu’oi na musamman a babban masallacin tarayya na Abuja, a lokacin rufe tafsiran watan Ramadana.
“Ina kiran ‘yan uwa musamman ‘yan Najeriya a ko ina a masallatai daban daban su yi addu’a na zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa ta mu, su yi addu’a Allah ya kawo mana mafita kan yadda za a warware wadannan matsaloli da su ka dame mu na tsaro a wannan kasa.” In ji Na’ibin limamin babban masallacin, Dr. Kabir Adam.
A wani bangaren, shugabannin al’uma sun kuma yi kira da a gujewa yiwa shugabanni mummunar addu’a domin karshen ta za ta iya dawowa kan masu yin irin wannan addu’a.
“Duk lokacin da mutum ya roki Allah ya halakar da shugabansa to ya yi ganganci.” In ji Dr. Suraj Sabo Keffi.
Ya kuma yi misali da cewa, yin irin wannan addu’a tamkar mutum yana cikin mota ne ya roki Allah ya sa direban ya makance.
“To kaga haka ai ya janyo wa kansa matsala, shi ya sa mu ke cewa mu rika yiwa shugabannin addu’a kuma mu kara juriyar hakuri, domin ba zai yiwu gyaran da muke so a same shi a wata daya ko biyu ko uku kai koma a shekara ba.” Dr. Keffi ya kara da cewa.
Ga karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya: