Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Na Cusa Kananan Yara a Cikin Mayakanta


Rundunar dakarun Kasashen yankin tafkin Chadi ta yi karin bayani dangane da yadda mayakan Boko Haram ke amfani da yara kanana a matsayin sojoji.

Kakakin rundunar Kanar Timothy Antiga ya shaidawa muryar Amurka cewa, bayanan sirri da aka tattaro sun tabbatar da hakan, yayinda wadansu mazauna yankin da kungiyoyi suka jadada hakan.

Kanar Antiga yace suma kansu sojojin sun tabbatar da haka yayin da suka wallafa hotunan wasu yara kanana da aka sanya su cikin aikin sojin dauke da manyan bindigogi.

Rundunar a yankin tafkin chadin tace wannan faruwa ne bayan da a baya kungiyar boko haram tayi ta sace yan mata dalibai, tana cin zarafin mata da ma kashe mutane fararar hula da basu ji ba basu gani ba.

ABUJA: Babban kwamandan rundunar hadin gwuiwa na sojojin yankin tafkin Chadi Manjo Janar Irabor
ABUJA: Babban kwamandan rundunar hadin gwuiwa na sojojin yankin tafkin Chadi Manjo Janar Irabor

Rundunar dakarun tafkin chadin tace sanya kananan yara aikin soji na zuwa ne ganin yanzu dakaru sun wargaza yan Boko Haram din a yankin al'amarin da ya sa da dama daga cikin mayakanta suka mika wuya ga dakarun MNJTF.

Sojojin yankin tafkin chadin suka ce sanya yara aikin soja ya sabawa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya kan kare kananan yara, don haka sun nemi majalisar tayi Allah wadai da hakan , kana tace a nata bangaren zata matsa kaimi wajen kawo karshen yan ta'addan.

Tuni dai masu rajin kare hakkin yara suke nuna rashin jin dadi bisa irin wannan sabon salo na yan ta'addan.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti

Ana Sa Kananan Yara Aikin Soji a Yankin Tafkin Chadi:4:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG