Jawabin karshe na shugaban Hukumar Zaben Najeriya (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, gabannin zaben 2019, wanda shi ne ya kara wa shekarar tagomashin tarihi a Najeriya. Duk da haka sai da hukumar zaben ta kasa cika alkawarinta na kauce wa dage zaben, inda Yakubu ya sanar da dage zaben daga ranar 16 zuwa 23 ga watan Fabrairu.
Wani muhimmin lamari shi ne yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da yadda a ke ganinsa a matsayin wanda ba ya sauya duk wanda ya nada sai ya yi murabus don samun sarauta kamar na tsohon Ministan Muhalli Usman Jibrin, wanda ya gaji sarautar Nassarawa, da Barista Ocholi wanda ya yi hatsari kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya riga mu gidan gaskiya, inda kafin maye gurbinsa sai da a ka share kusan shekara.
Dawowar Shugaban kan mulki a karo na biyu ya ajiye kadan daga cikinministocinsa na baya irinsu Mansur Dan Ali, Solomon Dalung, Isasc Adewole, Abdulrahman Dambazau da sauran su, ya shigo da sabbi irin su Isa Pantami da tsohuwar ma'ajiyar jam'iyyar sa ta CPC Sadiya Umar Farouk, wacce a ka yayata cewa Shugaba Buhari zai aureta amma hakan ya zama jita-jita.
A bangaren shari'a bayan korar karar kalubalantar ayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 2019, PDP,ta bakin kakakin kamfe din ta, Buba Galadima, ta ce bayan kotun kolin ta garzaya wata kotun.
A bangaren sarauta, bayan takaddama da hukuncin kotu, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya samu amincewar majalisa kan batun kirkirar sabbin masarautu 4, inda Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu ya amince da jagorantar majalisar sarakunan. Gwamnatin Kano na da matsayar shigar dattawa lamarin ba zai sauya dokar sabbin masarautun ba.
Kungiyar 'yan Shi’a ta IMN karkashin Malam Ibrahim El-zakzaky na cigaba da dagewa kan a sako jagoranta duk da haramta kungiyar da kotu ta yi bisa bukatar gwamnatin Najeriya.
Yayin da masu sharhi ke cewa matsin lambar Amurka ne ya sa gwamnatin Najeriya sake Kanar Sambo Dasuki, da Omoyele Sowore kan beli, Ministan shari'a Abubakar Malami na cewa a'a hakan ya biyo bayan bitar shari'ar da a ke yi ne.
Daga karshe hukumar EFCC ta samu izinin kotu na tsare tsohon Ministan shari'a Bello Adoke wanda ya shigo Najeriya daga Hadaddiyar Daular Larabawa inda ya ke fuskantar almundahanar sayar da rijiyar man fetur ta Malabu kan dala biliyan 1.3.
Saurari rahoto cikin sauti.
Facebook Forum