Birnin New York yace zai sake horad da jami'an yan sanda dubu ashirin. Birnin ya bada wannan sanarwa ce, bayan da gungun mutane dake yanke shawara, akan ko ya dace a gurfanar da wani gaban kuliya, suka yanke shawarar cewa ba zasu hukunta wani jami'in yan sanda bature daya shake wani bakar fata har ya mutu.
Jiya Alhamis magajin garin birnin Bill de Blasio yace yana da muhimmanci yan sanda su gudanar da aiyukansu ba tare da sun nuna bambamci ba.
Wani jami'in 'yan sanda mai suna Banjamin Tucker yace ba'a mu'amalla yadda ya kamata tsakanin yan sanda da jama'ar birnin miliyan takwas da dubu dari hudu. Yace za'a kare shirin sake bada horon na kwanaki uku a watan Yuni.
A ranar Laraba shugabanin hankoron kare hakkin tsiraru suka yi Allajh wadai da shawarar da aka yanke na kin hukunta jar fatan daya shake wani bakar fata har lahira. Al'amarin na birni New York yana daya daga cikin al'amurran da suke faruwa da yan sanda suke kashe bakar fata da ake da ayar tambaya akan irin wadannan kashe kashen.