Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Gano Wasu Na Amfani Da Kwayar Nitazenes A Afirka


Wani matashi na shan tabar kwayar kush, mai nau'in wiwi da ake hada wa da muggan kwayoyin Fentanyl da Tramadol da kuma kwayoyin Formaldehyde, a Freetown, kasar Sierra Leone, Afrilu 29, 2024. (Reuters)
Wani matashi na shan tabar kwayar kush, mai nau'in wiwi da ake hada wa da muggan kwayoyin Fentanyl da Tramadol da kuma kwayoyin Formaldehyde, a Freetown, kasar Sierra Leone, Afrilu 29, 2024. (Reuters)

A karon farko an gano cewa wasu mutane a nahiyar Afirka na amfani da muguwar kwayar Nitazenes dangin opiod, a cewar wani rahoto da kungiyar yaki da manyan laifuka ta kasa da kasa mai zaman kanta da ake kira Global Initiative Against Transnational Organized Crime ta fidda.

WASHINGTON, D. C. - An dade ana amfani da kwayar Nitazenes a kasashen Yammacin duniya da kuma nahiyar Asiya, wadda aka alakanta ta da mace-mace sakamakon shan kwayar fiye da kima. Karfin wasu daga cikin nau’in kwayar na iya linkawa har kusan sau 100 fiye da karfin kwayar Heroin, hakazalika har kusan sau 10 fiye da kwayar Fentanyl, abin da ke nufin ko da kadan masu amfani da kwayar suka sha zata yi musu tasiri, abin da zai sanya su cikin hadarin shan ta fiye da kima da ma mutuwa.

Rahoton ya mayar da hankali kan kasar Saliyo da Guinea-Bissau kuma an yi shi ne bisa ga gwajin sinadarin Kush, wani nau'in ganyen wiwi da ake hadawa da kwayoyi kamar Fentanyl da Tramadol da kuma sinadarai kamar Formaldehyde. Masu bincike sun gano cewa a Saliyo, kashi 83 cikin 100 na samfurin kwayar an gano yana dauke da Nitazenes, yayin da a Guinea-Bissau kuma kashi 55 cikin 100.

Yawancin matasa a Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka sun zama masu shaye-shayen kwayoyi sosai, inda tsakanin kashi 5.2 cikin 100 zuwa 13.5 cikin 100 ke amfani da tabar wiwi, haramtaccen maganin da aka fi amfani da shi a Nahiyar, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG