Masu bincike a birnin Dallas na jahar Texas, za su binciki rayuwar dan bindigar nan da ya kashe 'yansanda biyar a makon jiya.
"Idan ba mu yi binciken kwakwab ba," a cewar shugaban 'yan sandan Dalas, "ba zan gamsu" da cewa wai babu hannun wasu karin mutanen ba, "saboda mu tabbata babu abin da bamu bincika ba."
Ya ce hukumar 'yansanda na nazarin hotunan bidiyo wajen 170 daga kamarorin da 'yan sanda su ka makala jinkinsu, da kuma kamarorin da ke gaban motocin 'yansandan da kuma faya-fayen bidiyo daga kantunan da ke wajen, da kuma kamarorin tsaro da ke gefen hanyoyin wurin da hare-haren su ka auka. Baya ga jami'an 'yansanda biyar din da aka kashe a wannan al'amarin, wasu 'yansandan kuma tara da wasu farar hula sun samu raunuka.
Brown ya ce 'yan sanda wajen 11 ne su ka auna Micha Johnson da bindigoginsu, sannan wasu kuma biyu su ka sarrafa na'urar da aka samar akan kudi dala 151,000, wadda ta hallaka wanda ake zargin.
An samu abubuwan hada bam da wani dan kundi haka lokacin da aka binciki gidan Johnson. Jami'an tsaro sun ce babu wani bayanin da ke nuna cewa an taba samun Johnson da laifi a baya.