Gates wanda ya kaddamar da shirin allurar rigakafi na kasa, (NRISP), jiya a Abuja, yace, “babu abu mai mahimmanci a sashin lafiya na Nigeriya da ya wuce baiwa yara da sauran mutane allurar rigakafi domin kiyaye cututtuka."
Gates yayi bayanin cewa yadda shirye shiryen allurar rigakafi ke tafiya babu sauri, yadda yace “allurar rigakafi bata tafi hanyar da ta kamata ba.”
Ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu, yace sabon shirin ya kara kokarin gwamnati wajen kiyaye cututtukan da zata iya kiyayewa tawurin shirin yin rigakafi mai nagari.
Chukwu ya lura cewa bayan cututtuka kamar cutar shan inna da atini sun ci gaba da kawo kalubale, gwamnati na kokarin shiri da zai kawo sakamako mai dorewa.
Shugaban kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kara kwarin gwuiwar ‘yan majalisar dokoki na kasa da su kara kokari wajen aiwatar da dokar lafiya da kuma su tabbatar da cikakken asusu domin sashin lafiya.
Sakataren sashin inganta lafiya na kasa, Dr. Ado Muhammad yace sabon shirin ya tanada cikakken bayanai da ake bukata da kuma ingantaccen shirin allurar rigakafi.
Wakilin kungiyar GAVI, Dr Mercy Ahun yace wannan kungiyar ta “mika kai ga shirin allurar rigakafi a Nigeriya kuma tana sa ran Karin samar da sabobin alluran rigakafin da sabobin kayan aiki na lafiya nan gaba."
"Nigeriya tana baya wajen daidaituwar samar da allurar rigakafi a gidajen masu kudi inda yara fiye da 9 suke samun allura idan an kwatanta da na gidajen talakawa yaro daya kawai yake samun allurar."
Wannan shirin ya samu hallatar Sultan na Sokoto, Mai girma, Alhaji Sa'ad Abubakar, Asusun tallafawa yara, hukumar lafiya ta duniya da sauransu.