Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Saukin Yaduwar Cutar Kwalara a Jihar Plato


Ana lura da jama'a masu fama da cutar Kwalara
Ana lura da jama'a masu fama da cutar Kwalara

Gwamnatin jihar Plato ta dauki matakan tsabtar mahali a garin Namu dake jihar, inda aka sami rahotonin samun saukin yaduwar cutar kwalara.

Gwamnatin jihar Plato ta dauki matakan tsabtar mahali a garin Namu dake jihar, inda aka sami rahotonin samun saukin yaduwar cutar kwalara. A sami wanan rahoton bayan wata guda da mutane wajen tara suka rasa rayukan su.

An bayanna cewa ma’aikatan hukumomi suna bi gida gida suna gargadin dokokin kiwon lafiya.

Mutanen Namu, yayinda suke yin farin cikin samun saukin yaduwar cutar kwalara a garin sun nuna damuwa game da yawan masu zuwa Namu daga jihar Nassarawa domin zama.

Wani mutumin Namu, Mohammed Iliyasu, yace, “Babar matsalar da muke fuskanta ita ce mutum zaka bar gidanka ka je ka zauna a wani wuri daban? Wanan babar matsala ce.”

Inji wani malami mai suna Adamu Ivenya, “Har yanzu ina nan a Namu, kuma inda zanje in sa kai na da iyali na babu shi. Gwamnati ta taimaka tayi mana abin da za su iya domin mu koma gida, musaman inda zamu sa kan mu.”

Dr. Raymond Juryit, likita mai kula da cututuka masu yaduwa a jihar Plato ya ce ya kamata mutane su lura kuma su bi dokokin da aka bayar domin kiyayewa daga cutar kwalara.

Zainab Babaji ce ta aiko da rahoton daga Jos.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG