Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Zai Gabatar Da Wasu Kudurori Masu Alaka Da Iyalai Masu Aiki


Joe Biden
Joe Biden

Dan takarar jam’iyyar Democrats a zaben shugaban kasar Amurka Joe Biden, na shirin gabatar da wasu jerin kudurorin tattalin arzikin kasa wadanda za su mayar da hankali kan iyalai masu aiki.

Hakan na zuwa ne yayin da ya ke ci gaba da gangamin neman zabensa, kwanaki 100 gabanin masu zabe su yanke shawarar wanda za su zaba tsakaninsa da shugaba Donald Trump.

Kwamitin yakin neman zaben Biden ya ce zai yi bayyanin yadda kudirin na sa zai samar da rukunin kwararun ma’aikata masu ba da kyakkyawar kulawa da suka dace da karni na 21 da kuma na Ilimi, daga cikin shirinsa na farfado da tattalin arzikin Amurka mai taken “Build Back Better”.

Shugaba Trump da Abokin hamayyarsa Joe Biden
Shugaba Trump da Abokin hamayyarsa Joe Biden

Zabukan da aka gudanar a baya-bayan nan sun nuna cewa Biden na gaba da Trump, ciki har da wata kididgar da Reuters ta gudanar kan mutanen da suka yi rajistar zabe ta internet wanda ya bayyana Biden na gaba da Trump da maki 10 cikin dari.

Dan takarar democrats din ya ba da cikakken bayanin wasu sassan kudirinsa na farfado da tattalin arziki a yayin da kuma ya ke sukan shirin Trump game da yadda yake tafiyar da al’amuran tattalin arzikin kasa.

Trump ya mayar da martani tare da bayyana kansa a matsayin dan takara mafi cancanta da bunkasa tattalin arziki, ya kuma bayyana Biden da cewa bashi da kwarewar da ake bukata.

Tun a farkon watan nan, Biden ya bayyana shirin samar da kamfanonin kere-kere da zai ci dala biliyan 700 wanda ya ce, zai samar da sabbin ayyukan yi miliyan 5 da za su taimaka wajen magance matsalar rashin aikin yi da ke dada ta’azara a wannan lokaci na annoba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG