Wa'din na kunshe a wata wasika ce da kungiyoyin matasan suka rubutawa dattawan arewa da shugabannin siyasa da na addini da masu fada aji sun ce lallai a mika rashin jin dadinsu ga shugaban kasa domin a ja kunnuwan matasan kadu masu gabas da suke hakikancewa akan dole sai an raba kasar a basu Biafra.
Yusuf Muhammad Fantani daya daga cikin wadanda suka sa hannu a wasikar kuma shugaban kungiyar daliban arewa yace ba zasu amince da irin cin mutunci da masu neman kasar Biafra su keyi yiwa 'yan arewa dake zaune a kudu maso gabas ba.Idan an raba kasar yau kabilar Igbo ce zata shiga halin lahaula walakawati.
Shi ma jagoran shugabanin kungiyoyin Hashiru Sharif yace batun zabe ne ya kawo wannan kace nace din. Inji shi wadanda suka fadi zabe ne suke harzuka matasan.
Elder Okoro daya daga cikin Ohaneze kungiyar kabilar Igbo zalla reshen Abuja yace mafita daya ce kuma Shugaba Buhari ya nunata. Ya ba Igbo dama su gina kasa tare da basu ministoci hudu. Saboda haka yana ganin zai kira gwamnatocin jihohinsu su ja kunnuwan matasan domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki.
Ga karin bayani.