Yayin da hukumomin a Jamhuriyar Benin suka katse hanyoyin amfani da yanar gizon kasar a lokacin zaben 'yan majalisa da aka yi ranar Lahadi, kasar ta zama kasa ta 9 a inda gwamanati ta dauki irin wannan matakin a wannan shekarar.
Dakatar da hanyoyin yanar gizon da aka yi ya kai na sa’oi ko kwanaki kuma zai iya shafar wasu ayyuka na yanar gizon din ko kuma gaba daya yanar gizon.
Gwamanatoci ba kasafai su ke fitowa suyi bayanin dakatarwar ba, amma idan suka yi, suna maida hanakali ne kan bukatar tsaro da kuma tabbatar da doka ga al’umma. Rufewar yawanci takan zo da rashin amincewa, zanga-zanga da kuma zabe.
Amma bayanai daga NetBlock Group, wata kungiya mai lura da yancin yin amfani da yanar gizo da saka idanu toshewar hanyoyinta a duniya, ta nuna tasirin irin wannan lamarin akan tattalin arzikin kasashen da abin ya shafa ko da kuwa dakilewar hanyoyin na karamin lokaci ne.
Facebook Forum