A Najeriya mahawara ta kaure a tsakanin manazarta kan batun raba ayyuka a asirce da a yanzu haka ya kunno kai a Majalisar dattawa, inda aka yi zargin cewa ana raba wa Sanatoci kujerun ayyuka domin su kai mazabunsu a maimakon bin diddigi da ka'ida wajen raba su.
Wannan batu da ya ja hankalin manazartan ya faru ne a Majalisar Dattawa inda aka yi zargin cewa ana rabawa 'yan Majalisar kujerun ayyuka daga Ma'aikatun Gwamnati da Hukumominsu musamman ma daga Hukumar kula da haraji ta kasa.
Wani abu da mai fashin baki a harkokin siyasa da zamantakewa Mohammaed Ishaq Usman ya bayyana shi a matsayin wani abu da ya faro tun zamanin soja har ya zuwa wannan lokaci na siyasa, har ya so ya shafi mulkin Buhari a wa'adinsa na farko inda aka jima ba a samu kafa ma'aikatun Gwamnati da wuri ba.
Batun na uwa amurhu ko akasin haka ya sa Malam Abdulkarim Gambo daga Jihar Adamawa tuna baya, inda ya ce a da sai kana da takardu kuma a tantance ka sannan a ba ka aiki a bisa cancanta ba wai don uban gida ko uwa a murhu ko addini ba, tare da yin shawara da a koma wannan lokacin idan ana so abubuwa su yi kyau a kasa.
A na shi nazarin, kwararre a fannin kundin tsarin kasa, Barista mainasa Kogo Ibrahim Umar ya ce, a shari'ance za a ce zargi ne, amma kuma in aka tabbatar da gaskiyan al'amarin, to an yi wa kudin tsarin kasa karan tsaye kuma a irin wannan hali dole ne doka ta hau kan mutumin da ya yi amfani da mukaminsa wajen kyautata wa waninsa ko dangin sa.
To sai dai mai magana da yawun Majalisar Dattawa Sanata Adebayo Adeyeye ya tabbatar wa manema labarai cewa kwamitinsa zai yi bincike bayan ya zauna da Shugabanin Majalisar.
Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda daga Abuja: