A ranar jajiberin da shugaba Donald Trump zai kama hanyarsa ta zuwa nahiyar Asiya, Fadar Shugaban kasar ta White House, ta ce batun barazanar da Pyongyang ke yi shi ne zai zamanto muhimmin batu da za a tattauna da shugabannin yankin, sannan kwance damarar makamin nukiliyan Korea ta arewa shine zabi kadai da za a amince da shi.
Mai bai wa shugaba Trump shawara kan harkar tsaro, H.R McMaster, ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi amfani da iya karfinta wajen maida martani akan barzanar da Korea ta arewan ke yi.
A tsakanin ranaku bakwai da takwas na wannan wata na Nuwamba, ake sa ran shugaba Trump zai kai ziyara Korea ta Kudu, wacce abokiyar hammaya ce ga takwararta ta arewa.
Ziyarar ta Korea ta Kudu za ta kasance zango na biyu da shugaba Trump zai yada cikin kwanaki 12 da zai kwashe yana ziyarar kasashe biyar a nahiyar.
Tattaunawar da shugaban na Amurka zai yi da takwaran aikinsa na Korea ta Kudu, Moon Jae-in da wasu shugabannin duniya, za ta fi maida hankali ne kan neman amsar tambayar yadda za a tunkari shirin gina makaman nukiliyan da na linzami da Pyongyang ke yi.
Ana dai ci gaba da samun yanayi na ta da jijiyar wuya a tsakanin kasashen biyu da ke bangarorin yankin tekun Pacific, lamarin da Shugaba Trump yake ma kallon muhimmin batu wajen ganin ya cimma burinsa na kawar da barazanar da Korea ta Arewa ke yi wa Amurka da makaman kare dangi.
Facebook Forum