Akan wannan batun ne Aliyu Mustaphan Sokoto na Sashen Hausa a Muryar Amurka ya nemi mai baiwa Jonathan shawara akan harkokin siyasa, Farfesa Rufa’I Alkali.
Rufa’I Alkali yace “yanzu hukumar zabe ta fito da jaddawalin shirye-shiryen zabe da za’a yi a shekara ta 2015, kuma jam’iyyar mu ta PDP ta fito da nata jaddawali na shirye-shiryen zabubbuka da za’a yi anan gaba. Saboda haka za’a ce siyasa ne da za’a yi nan gaba, ya dauki harama”.
“Tunda yanzu siyasa ya dauki harama, to babu abunda baza ka gani ba, kuma babu abunda baza ka jiba. ‘Yan hamayya, zasu ringa bullowa da maganganu daban-daban, da kuma wadanda zasu yiwa shugaban kasa batanci. Naji wannan batu, kuma ‘yan hamayya ne suka bullo da wannan magana, saboda suna gani idan ba haka sukayi ba, baza su iya karya wannan tafiya ba”, inji Mr. Alkali.
Aliyu Mustapha ya tunatar da Farfesa Alkali cewa ba shugaba Jonathan ne kawai aka fito da yawan arzikinshi ba, shugaban Angola ma shine yafi kowani shugaban Afirka arziki. Shima wannan ‘yan siyasan Najeriya suka fitar da wannan labara? Shine Farfesan yace “baka tambaye ni akan shugaban Angola ba, akan shugaban Najeriya ka tambaya. Bazan iya sanin yadda rayuwar shugaban Angola take ba”.