Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tunatar da iyayen ‘yan matan da aka sace a makarantar Chibok da ke jihar Borno cewa, bai manta da ‘ya’yansu ba.
Shugaban Najeriya ya bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun daya daga cikin masu magana da yawunsa, Garba Shehu.
A yau ake jimamin cika shekaru biyar cif da sace ‘yan matan.
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, mayakan Boko Haram suka kai hari a makarantar sakandare ta Chibok, inda suka sace ‘yan mata sama da 200.
A cikin sanarwar, shugaba Buhari ya ce, ya san cewa, saboda alkawarin da ya ma al’umar garin Chibok na kubutar da ‘ya’yansu ne, ya sa suka sake zabensa a watan Fabrairu.
Buhari ya ba da kwarin gwiwar cewa, har yanzu gwamnatinsa na bibiyan batun ‘ya’yan na su.
“Ana ci gaba d daukan matakai daban daban, domin ganin an sako ‘yan matan Chibok da duk sauran mutanen da kungiyar Boko Haram ke garkuwa da su, ciki har da Leah Sharibu.”
Dangane da batun Sharibu, matashiyar nan da ita ma aka sace ta a baya-bayan nan, a garin Dapchi da ke jihar Yobe tare da wasu dalibai da aka riga aka sako, sanarwar ta nuna cewa, masu shiga tsakani kan tattaunawar ganin an sako dalibar, suna ba da rahotannin da ke nuna cewa ana samun ci gaba.
“Rahotannin da muke samu na cewa, akasin da aka samu shi ne, mayakan kungiyar ta Boko suna nuna fargaba ne dangane da kasancewar dakarun Najeriya a yankin a 'yan kwanakin nan.”