Buhari ya yi wannan magana ce a lokacin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, bayan ganawarsa da shugaba Trump.
A cewar Buhari yanzu wasu jihohin Najeriya ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu, balle kuma a ce za su iya daukan nauyin rundunar ‘yan sandansu.
Shugaban dai ya ce a yanzu hankalinsa bai kwanta ba akan barin jihohi su mallaki ‘yan sandan kansu ba, amma sai an duba tsarin mulki domin tabbatar da abin da doka ta tsara kafin a san abin da za ayi.
Haka kuma shugaba Buhari ya amince da daukar ma'aikatan 'yan sanda 6,000 a matsayin wani ɓangare na matakan da za su magance matsalolin tsaro na kasa da suka hada da manoma da makiyaya a fadin kasar.
Domin karin bayani saurari kadan daga cikin hirar da aka yi da shugaba Buhari.
Facebook Forum