Bayanin da ma’aikatar tsaron Afghanistan ta bayar yau juma’a yace ba’a rasa ran farar hula ko guda ba a harin. Bam din mai nauyin Kilogram 10,000 wanda ake kira da ”Uwar Bama Bamai” an jefa shine a kan sansanin ‘yan 'kungiyar ISIS da ke Kudu maso gabashin Gundumar Nangarhar ta Afghanistan jiya Alhamis.
Ofishin shugaban 'kasar Afghanistan Ashraf Ghani yace an gudanar da wannan hari ne da hadin gwiwar Jami’an tsaron Afhganistan . Haka kuma ya kara da cewa Dakarun Afghanistan na hada kai da rundunar Turai ta NATO domin 'karfafa ya'kin da ake da kungiyoyin ‘Yan tsagerun.
Tsohon shugaban 'kasar Afghanistan Hamid Karzai yayi Allah wadai da amfani da wannna katafaren Bam akan 'kasar Afghanistan.
Facebook Forum