‘Yan wasan Ferroviario de Maputo na kasar Mozambique sun doke AS Douanes na kasar Senegal da ci 88-74 a gasar zakarun kwallon kwando ta nahiyar Afirka da ake yi a Kigali, Rawanda.
'Yan wasan na Mozambique sun nuna kwarewa sama da takwarorin karawarsu na Senegal wadanda mafi akasarinsu matasa ne kamar yadda rahotanni suka nuna.
Gasar ta BAL ta shiga kwana na biyar kenan a ranar Alhamis, inda kungiyoyi 12 ke neman lashe kofin wannan gasa wacce ake yin ta a karon farko.
An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.
Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar.
Sauran kasashen sun hada da Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.
Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka. Ga jerin sunayen kungiyoyin da zakarun ‘yan wasansu da suka fi fice.