Kungiyoyin Alkalan shari’a da ta lauyoyi a Jamhuriyyar Nijer sun ci gaba da matsawa gwamnatin kasar lamba dangane da batun karkata akalar wasu dubban miliyoyin cfa a ma’aikatar tsaron Kasar. Kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin kasar akan ganin an gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifin.
Gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar cewa har yanzu masu bincike ba su kamalla hada rahoton binciken su ba na dindindin akan wannan badakala, inda ta ce, shine ya haddasa tsaiko wajen gabatar da lamarin ga kotu.
Kungiyar alkalan shari’a SAMAN na daga cikin kungiyoyin da suka yi tur da wannan al’amari, bayan da gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar.
Sakataren yada labaran kungiyar, Mai shari’a Zakari Yaou Mahamadou, ya ce, in ana so shari’a ta ci gaba da aikinta, dole ne sai an mutunta shari’a kuma an bi dokokin tsarin mulkin kasar.
Kungiyar matasan lauyoyi ta AJAN, it ma ta soki matakin da gwamnatin kasar ta dauka.
Ministan shari’a Marou Amadou, ya ce, a ka’ida ba a gabatar wa alkali mai tuhuma rahoton wucin gadi sai idan an kammala bincike.
Abba Hassan na kungiyar fafitika ta AEC, masu rajin kare dimokradiya ya ce, irin wannan badakala a ma’aikatar tsaro tamkar wata barazana ce ga dorewar dimokradiya a kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum