Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Taron Mayan Shugabannin PDP Kamar Yadda Aka yi Zato


Makon da ya gabata ake ta raderadib cewa manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP zasu yi taro inda zasu dauki wasu matakai na musamman.

Ba kamar yadda wasu jaridu suka sha fada ba cewa masu ruwa da tsaki a cikin jam'iyyar PDP zasu yi taro yau, to amma batun ba haka yake ba.

Mataimakin jami'in labarun jam'iyyar Barrister Abdullahi Jalo ya ce babu batun taron.To sai dai masu matsa lambar sai Bamanga Tukur ya yi murabus suna cigaba da yi. Jalo yana ganin bukatarsu tamkar mafarki ne kawai. Ya ce wai jam'iyyar ta lalace ne bata da shugabannin ke nan har ma idan zata yi taro irin wanda aka ambata ba za'a yi sanarwaba a kafofin labaru kuma shugabanta ba zai sani ba. Masu son su kawo fitina su ne suke yayata batun taron da babu shi.

Barrister Abdullahi Jalo ya ja kunnen masu tunanin PDP ta shiga wani halin nakasa cewa a bar yiwa biri murna idan jeji ya kama wuta sai wutar ta lafa. 'Yan adawa suke yiwa PDP sharri. Shi ma dan kwamitin zartaswar jam'iyyar Isa Tafida Masindi gani yake zai yi wuya Bamanga Tukur ya sauka daga mukaminsa, kuma da alamun Jonathan zai yi takara a zaben 2015. To sai dai Isa Tafida Masindi na ganin ba 'yan jam'iyyar tikitin tsayawa takara kai tsaye zai kawo cikas matukar ba'a yi zaben fida kwani ba.

Ya ce Allah ya kawo lokacin da har uban gidan ya sani kuma ya ji a jijiknsa cewa 'ya'yansa sun shiga rigima. 'Ya'yan ma ba wai suna jiran rasuwar uban nasu ba ne su kwashi kayan gado, a'a tun yana da rai suna kwasan kayan sun kai wasu wurare suna bazawa. Ya ce gwamnoni suna tafiya. 'Yan wakilai suna tafiya. Ya ce amma har yanzu shi Tafida bai karaya ba. Amma matsalar da PDP zata shiga da fita zai yi mata wuya shi ne bada tikitin tsayawa zabe ba tare da yin zaben fitar da gwani ba. Domin duk wanda yake neman kofa aka rufeta to dole ne ya je inda kofa na bude.

Dan majalisa kuma dan PDP Aminu Kurfi dake shirin tsayawa takara ya yi watsi da batun bada tikiti ba tare da yin zaben fitar da gwani ba. Ya ce 'yan kwamitin zartaswar jam'iyyar babu wanda ya isa ya yi hakan.

To saidai PDP ta fitar da wata sanarwa inda ta ce jam'iyyar APC tana son kawo siyasar addini kamar ta 'yanuwa Musulmi na kasar Masar ta Mohammed Morsi ta yi yunkurin kawowa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG