Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma yana ci gaba da samun matsin lamba daga cikin-da-wajen jam'iyyar ANC mai mulkin kasar, cewa yayi murabus. Shugaban yana tsaka mai wuya dangane da zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka yi masa katutu.
Mataimakin shugaban kasa, kuma sabon shugaban jam'iyyar ta ANC Cyril Rasmaphosa, ya gayawa taron jama'a a bikin cika shekaru 28 da sakin Nelson mandela daga kurkuku a Lahadin nan cewa, su kara hakuri ana ci gaba da tattaunawa dangane da makomar shugaban na Afirka ta kudu.
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Dr. Abdullahi Yusuf, na jami'ar Pretoria dake Afrika ta kudu, yace cikin batutuwa da ake jin sune suke hana Jacob Zuma sauka, sun hada harda neman kariya daga hukunci idan ya sauka.
Dr. Abdullahi yace, kwan-gaba-kwan-baya da ake yi kan batun saukar sa Zuma ya shafi harkokin yau da kullum.
Ga karin bayani.
Facebook Forum