Babbar jami’ar cibiyar kare hakin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta yi kira ga shugabannin siyasa da na addini a Najeriya su hada hannu wajen shaow kan tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.
A cikin sanarwar da ta bayar yau alhamis, Pillay tace yana da muhimmanci matuka shugabannin Musulmi da Kirista su fita karara su yi allah wadai da tashin hankalin, da ya hada da hare haren ramuwar gayya. Bisa ga cewarta daukar wannan matakin zai taimaka wajen hana kara bazuwar tashin hankalin.
Ta bayyana haka ne kwana daya bayanda shugaban kungiyar mayakan Boko Haram yay i alkawarin kara kai hare hare.
Hukumomi a Najeriya suna dorawa kungiyar alhakin asarar daruruwan rayuka a hare haren da suka rika kaiwa na tsawon watanni goma sha takwas. Kungiyar ta dauki alhakin hare haren da aka kai da dama da suka hada da harin da aka kai kan wata majami’a kusa da Abuja ranar Kirsimeti da ya yi sanadin kashe sama da mutane 30.
Pillay tace idan aka tabbatar membobin kungiyar Boko Haram suna kaiwa farin kaya hari, za a iya samunsu da laifin cin mutumcin bil’adama.
Kungiyar tana nema a kafa shari’ar addinin Islama a duk fadin Najeriya. Ta kuma gargadi Kiristoci dake arewacin kasar da musulmi suka fi rinjaye da su bar yankin.