Kungiyoyin kwadagon Nigeria dake jagorancin yaje-yajen aiyukkan da ake a kasar baki daya don nuna rashin yarda da janye tallafin man fetur, sunce zasu dakatarda yajin aikin nasu – amma na kwannaki biyu na karshen makon nan kawai da za’a shiga. A yau ne kungiyar kwadago ta Nigeria ta NLC ta bada sanarwar cewa ma’aikata na iya jingine yajin aikin nasu a rannakun Assabar da Lahadi, amma su shiryawa komawa yajin daga ranar Litinin mai zuwa. Kungiyoyin kwadagon sun bada hujjoji daban-daban akan dalilinsu na neman dakatarda yajin, wanda suka hada da dayarsu dake cewa tana son jama’a su fita su mike kafa ne, a huta kana a dawo cikin kuzari ranar Litinin. An dai ci gaba da wannan yajin aikin a Jumu’a – rana ta biyar da fara shi – bayanda aka kasa cimma matsaya a tattaunawar da ake a tsakanin jagabannin kwadagon da wakilan gwamnati akan ko a dawo da tsohon farashin na man fetur. A ran 1 ga watan nan na Janairun nan ne dai gwamnatin ta Nigeria ta janye tallafin man fetur, wanda yassa farashinsa ya ribanya fiyeda sau biyu.
An dakatarda yajin aiki a Nigeria
- Aliyu Mustapha
![Gungun masu zanga zanga gama gari a najeriya sakamakon janye tallafin mai. Wan nan gangamin a legas aka yi.](https://gdb.voanews.com/ec581c28-f991-45bf-9471-614fa6279e37_w250_r1_s.jpg)
Kungiyoyin kwadago na Nigeria zasu dakatarda yajin aiki na kwannaki biyu.