ABUJA, NIGERIA - Sanata Abdullahi Adamu ya ce ba ya shakkar a gudanar da zabe a tsakanin sa da sauran 'yan takarar neman shugabancin APC a karshen makwan nan.
Tun fitowar Adamu neman jagorancin APC da shi ne kusan na karshe a bayyana wannan aniya, a ke cewa shugaba Buhari ne ya mara masa baya kasancewar sa mai yawan shekaru da rashin shakkar daukar matakai.
Tsohon gwamnan na Nassarawa bai fito kai tsaye ya ce shugaba Buhari na mara masa baya ba, amma ya yi jirwaye mai kamar wanka.
Duk da tura takarar yankin arewa ta tsakiya, akalla Abdullahi Adamu na da abokin takara mai karfi daga Jihar sa ta Nassarawa, tsohon gwamna Tanko Almakura.
Adamu ya ce a rayuwarsa ba ya fargabar fadawa kowa gaskiya sai dai sanin furucin da zai yi amfani da shi bisa darajar wanda ya ke yi wa magana.
Daya daga 'yan takarar Sanata Sani Musa 313 daga Neja ya ce ba su da tabbacin shugaban kasa ya marawa wani dan takara baya.
Shi kuma tsohon gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari da ke takarar ya ce bai amince da batun tura takarar arewa ta tsakiya ba.
Amma dan majalisar wakilai Abdulrazak Namdas na da kwarin guiwar za a sulhunta wajen fitar da sabon shugaban na APC.
Kimanin wakilai 4000 za su halarci babban taron na APC ranar Asabar din nan a dandalin taro na EAGLE da ke Abuja.
Saurari rahoto cikin sauti daga Saleh Shehu Ashaka: