Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren Kungiyar OPEC Mai Barin Gado Mohammad Barkindo Ya Rasu


 Mohammed Sanusi Barkindo
Mohammed Sanusi Barkindo

Babban sakataren kungiyar OPEC mai barin gado, Muhammad Sanusi Barkindo, ya mutu a daren jiya Talata kasa da wata guda kafin ya yi ritaya.

Daraktan gudanarwa na kamfanin NNPC, Mele Kyari ne ya sanar da rasuwar tasa a shafin sa na Twitter da safiyar yau sai dai bai bayyana sanadin mutuwar tasa ba.

Sanarwar tace: “Mun yi rashin mai girma Dakta Muhammad Sanusi Barkindo. Ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren jiya 5 ga watan Yuli, 2022 . Babu shakka wannna babban rashi ne ga danginsa, da kamfanin NNPC, da kasarmu Najeriya, da kungiyar OPEC, da kuma kungiyar makamashi ta duniya. Za a sanar da sanar da shirye-shiryen jana’izar shi nan ba da dadewa ba.”

Ziyarar Mohammed Sanusi Barkindo Sashen Hausa Na Murayar Amurka
Ziyarar Mohammed Sanusi Barkindo Sashen Hausa Na Murayar Amurka

Dr Barkindo ya rasu yana da shekaru , 63 a duniya.

An nada Dr Barkindo a matsayin Sakatare Janar na OPEC a shekarar 2016 ya kasance dan Najeriya na hudu da ya rike wannan mukamin kuma mutum na 28 da ya rike matsayin.

Kafin zaben shi a matsayin Sakare Janar na OPEC, ya yi aiki a matsayin babban darektan kamfanin NNPC (GMD) tsakanin 2009 zuwa 2010.

Bayanai na nuni da cewa, jiya Talata marigayin ya yi wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bayyana cewa wa’adinsa na shekaru shida a matsayin magatakardan kungiyar ta OPEC ya zo karshe.

Ziyarar Mohammed Sanusi Barkindo Sashen Hausa Na Murayar Amurka
Ziyarar Mohammed Sanusi Barkindo Sashen Hausa Na Murayar Amurka

Baya ga ziyarar Aso Rock, Dr Barkindo ya kuma gabatar da jawabi ranar a taron mai da iskar gas na Najeriya da aka gudana a Abuja.

Barkindo ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin gwiwa tsakanin OPEC da kasashen da ba na OPEC ba kan daidaita kasuwannin mai, biyo bayan faduwar farashin mai a shekarar 2020.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta OPEC ta fitar, ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga daukacin iyalan kungiyar ta OPEC, masana'antar mai, da sauran kasashen duniya.

Jim kadan bayan wallafa sanarwar rasuwar sa mutane su ka fara aika sakon ta'aziya:

Taskar VOA Ta Sami Bakuncin Babban Sakatare Janar Na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC, Mohammad Sunusi Barkindo
please wait

No media source currently available

0:00 0:14:59 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG