Babban Atoni-janar din Amurka William Barr, ya yi watsi da kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa Ma’aikatar Shari’a ta binciki mutumin da ya gada, Barack Obama.
Barr ya ce bai tunanin Ma’aikatar ta Shari’a za ta binciki Obama ko mataimakinsa Joe Biden, game da cancantar binciken katsalandan din Rasha, wanda a yanzu ya zama wani abin takaddama.
“Game da Shugaba Obama da Mataimakin Shugaban Kasa Biden, ko da wani irin rawa suka taka, bisa ga bayanan da nake da su zuwa yau dai, ba na tunanin binciken da Mr. Durham ke yi, zai kai ga kaddamar da binciken zargin aikata manyan laifuka a kansu,” a cewar Barr a wani taron manema labarai.
Barr ya ce binciken da Ma’aikatar Shari’ar ta yi kan katsalandan din Rasha a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016 da zimmar taimaka ma Trump ya yi galaba kan Hillary Clinton, ya gudana ne cikin amfani da ikon hukuma ba bisa ka’aida ba, musamman ma ta bangaren jami’an tsaro a gwamnatin Obama.
Amma ya kafa hujja da wata shari’ar da Kotun Kolin Kasar ta yanke kwanan nan, wadda ake wa lakabi da tabargazar Bridgegate, wajen cewa ba wani laifi na amfani da ikon gwamnati ba bisa ka’ida ba kan zama babban laifi.
Facebook Forum